Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Shaidun gani da ido sun rawaito cewa: Jiragen leken asiri na Amurka da Birtaniya sun yi ta shawagi sararin samaniyar Qatar kafin a kai harin bayan nan kuma aka ji karar fashewar wasu abubuwa a birnin Dohar kasar Qatar.
Lokacin harin ta'addancin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai kan tawagar Hamas a Qatar
Makasudin harin ta sama shi ne kashe shugabannin Hamas da ke halartar wani taro domin mayar da martani ga bukatar Amurka na duba shirin tsagaita wuta.
Kamar yadda babban (memba na Hamas) Suhail Al-Hindi ya tabbatar: Muna nazarin shawarar Trump lokacin da aka jefa mana bam. Amurka ce ke da alhakin wannan harin.
Tashar talabijin ta Al-Mayadeen da Qatar ta Al-Araby, sun nakalto daga majiyoyi masu tushe cewa tawagar Hamas da ke tattaunawa a Doha ta tsallake rijiya da baya a yunkurin da Isra'ila ta yi na kashe su.
Jami'in Fadar White House sun tabbatar da cewa: Gwamnatin Trump na sane da harin da Isra'ila ta kai wa Qatar
Wani jami’in fadar White House da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa kafafen yada labaran Amurka da na duniya cewa an sanar da gwamnatin Trump kan lamarin kafin Isra’ila ta kai hari kan manyan jami’an Hamas a Qatar.
Jami'in na Amurka ya yi ikirarin cewa Isra'ila ta sanar da Amurka ne a lokacin da take harba makamin, don haka gwamnatin Trump ba ta da damar yin bincike kan lamarin.
Kamar yadda ita kasar Qatar a nata martanin ta dakatar da shiga tsakanin da ta ke tsakanin Isra'ila da Hamas a matsayin martani ga harin na yau.
Duk da rahotanni da dama daga majiyoyin labaran yahudawan sahyoniya kan rawar da Amurka ta taka a harin da aka kai Qatar a yau, ofishin Netanyahu ya fitar da wata sanarwa da ke cewa Isra'ila ta kai harin ne da kanta.
Har yanzu sojojin Isra'ila ba su tabbatar da sakamakon harin da aka kai a Doha ba.
Kamar yadda Al-Mayadeen ya ce: Kisan shugabannin Hamas bai yi nasara ba, amma wasu jami'an ofishin kungiyar sun yi shahada.
Your Comment